Adadin mutanen da aka kama sanadiyar tarzomar Faransa ya haura dubu biyu
Sama da mutane dubu 2 ne aka kama a Faransa, tun bayan tarzomar da ta biyo bayan kisan da 'yan sanda suka yi wa matashi Nahel, kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta sanar a yau Lahadi.
Wallafawa ranar:
Daren jiya Asabar wanda kuma shine na biyar a jerin dararen da aka faro zanga-zangar kisan matashin, hukumomin Faransa sun tabbatar da kama mutane 719.
Ma’aikatar kulada harkokin cikin gida ta kasar, ta ce ana kuma samun raguwar tarzomar da aka faro tun a ranar Talatar da ta gabata.
Ministan kulada harkokin cikin gida na Faransa Gerald Darmanin, a jiya Asabar ya sanar da shirin tura jami’an ‘yan sanda dubu 45 sassan kasar don kwantar da tarzomar a daren na Asabar.
A jiya ne dai aka binne matashin, inda ‘yan uwa da abokan arziki ke cike da alhinin rashinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu