Isa ga babban shafi

Gwamnatin Faransa ta ce an samu raguwar tarzomar da ta tashi a kasar

Hukumomin Faransa sun ce an samu saukin tarzomar da aka samu a kasar, bayan kwashe kwanaki hudu ana gudanar da zanga-zangar da ta biyo bayan kisan da dan sanda suka yi wa wani matashi.

An samu saukin tarzomar da ta biyo bayan kashe wani matashi da dan sanda ya yi a Faransa.
An samu saukin tarzomar da ta biyo bayan kashe wani matashi da dan sanda ya yi a Faransa. AP - Christophe Ena
Talla

Faransa ta girke jami’an tsaro dubu 45 da motoci masu sulke, yayin da jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka watsu a fadin kasar domin dakile tashe-tashen hankulan da ake yi kan mutuwar Nahel, wanda jami’an tsaro suka kashe a lokacin da aka tsaida shi don gudanar da binciken motarsa a wata unguwa da ke birnin Paris a ranar Talata.

Duk da kasancewar jami'an tsaro, masu zanga-zangar sun ci gaba da wawushe kayayyaki a daren Juma'a a biranen Lyon da Marseille da kuma Grenoble.

Haka nan masu zanga-zangar sun kuma kona motoci da wuraren zuba shara.

Sai dai a wata ziyara da ministan harkokin cikin gida na kasar Gerald Darmanin, ya kai Mantes-la-Jolie da ke yammacin birnin Paris a safiyar yau Asabar, ya bayyana cewa an samu saukin boren da ake yi a daren jiya, inda kuma aka kama karin mutane 471 a fadin kasar musamman a Marseille da Lyon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.