Isa ga babban shafi
RIKICIN ISRA'ILA DA HAMAS

Amurka na tufka da warwara game da batun tsagaita wuta a Gaza

Yayin da Isra'ila ke shirin kai farmaki ta kasa a Rafah, shugaban Amurka, Joe Biden, na ci gaba da jadadda bukatar tsagaita bude wuta na wucin gadi a yankunan Falasdinawa.

Shugaban Amurka, Joe Biden, lokacin da yake karbar bakuncin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin New York, ranar 20 ga Satumba, 2023.
Shugaban Amurka, Joe Biden, lokacin da yake karbar bakuncin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin New York, ranar 20 ga Satumba, 2023. AP - Susan Walsh
Talla

Jam'iyyarsa ta Democrats dai na na ci gaba da fuskantar suka daga ‘yan adawa, wadanda ke son tsagaita wuta ta dindindin a yakin da aka kashe kusan Palasdinawa 30,000.

Amurka ta yi watsi da daftarin kudirori uku na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan yakin Isra'ila da Hamas.

Na baya-bayan nan shine kin amincewa da kiraye-kirayen da ke neman tsagaita wuta domin kai agajin jin kai cikin gaggawa, amma a yanzu Washington ta gabatar da nata daftarin kudurin da ya tanadi kalmar tsagaita wuta.

Daftarin ya yi kira da a tsagaita bude wuta na wucin gadi a yakin Isra'ila da Hamas da ke da alaka da sakin mutanen da Hamas ke garkuwa da su da kuma adawa da wani babban farmaki da Isra'ila ke kai wa a Rafah.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta musanta duk wani zargin sauya magana kan rikicin Isra’ila da Hamas.

Masu suka dai na ganin Amurka na ci gama da yin amai tana lashewa game da rikicin na Isra’ila da Hamas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.