Isa ga babban shafi

Dubban Falasdinawa sun yi zanga-zanga kan ziyarar Blinken a Ramallah

Dubban Falasdinawa ne yau Laraba suka gudanar da wani gangami a Ramallah don nuna adawarsu da ziyarar sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a yankin yayin ziyarar da ya ke kaiwa gabas ta tsakiya dangane da yankin Isra’ila da zuwa yanzu ya kashe Falasdinawa fiye da dubu 23.

Sakataren wajen Amurka Antony Blinken tare da jagoran Falasdinawa Mahmoud Abbas Ramallah.
Sakataren wajen Amurka Antony Blinken tare da jagoran Falasdinawa Mahmoud Abbas Ramallah. REUTERS - EVELYN HOCKSTEIN
Talla

Galibin Falasdinawan sun rike allunan da ke dauke da rubutun ‘‘ba ma marabá da zuwanka Blinken’’, sun yi dafifi akan tituna gabanin jami’na tsaro su tarwatsa su.

Wannan ne ziyara ta biyu da Blinken ke kaiwa gabas ta tsakiya tun bayan faro yakin na Isra’ila a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da Hamas ta kai hare-hare kan iyakar kasar ta Yahudawa.

Wani batu da ya harzuka Falasdinawan shi ne yadda kalaman Blinken kai tsaye yayin ganawarsa da Benjamin Netanyahu ke jinjinawa Isra’ilan kan abin da ya kira murkushe Hamas.

A kalaman Blinken yayin ziyarar ya ce Isra’ila ta dauki matakin da zai kange ta daga ganin makamancin hare-haren Hamas na ranar 7 ga watan na Oktoba.

Har zuwa yanzu dai Amurka na ci gaba da taimakawa Isra’ila da tarin makaman da ta ke ci gaba da kai hare-hare yankin na Gaza da zuwan yanzu ta rushe fiye da kashi 80 na gine-ginensa ciki har da makarantu da asibitoci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.