Isa ga babban shafi

Amurka ta sake ayyana mayakan Houthi a matsayin 'yan ta'adda

Gwamnatin Amurka ta sake ayyana mayakan tawayen Houthi na Yemen masu samun goyon bayan Iran a matsayin 'yan ta'adda, bayan janye su daga cikin Bakin Kundin da ta yi a shekarar 2021.

Mayakan Houthi a kasar Yemen
Mayakan Houthi a kasar Yemen REUTERS - KHALED ABDULLAH
Talla

Yayin sanar da daukar matakin a hukumance, mai bai wa gwamnatin Amurka shawara kan tsaro Jake Sullivan, ya ce ayyana 'yan Houthin a matsayin 'yan ta'addan ba zai fara aiki ba sai bayan kwanaki 30, kuma idan har mayakan suka daina kai hare-hare a tekun Red Sea, a shirye Amurka take ta janye matakin da ta dauka a ranar Laraba.

A kwanakin baya bayan nan Amurka ta kaddamar da hare-hare kan mayakan Houthi a yankunan da suke iko da su a Yemen, matakin da ta ce martani ne a kan farmakin da suka rika kai wa kan jiragen ruwa a tekun Maliya.

A makon da ya gabata, mayakan Houthi suka sha alwashin kai hare-hare kan manyan jiragen ruwan dakon kaya da ke kan hanyar su ta shiga Isra'ila hari ba tare da la'akari da kasashen da suka fito ba, matakin da suka ce za su ci gaba da dauka muddin Isra'ila ba ta daina yi wa Falasdinawa kisan kare dangi ba a Zirin Gaza.

A karkashin gwamnatin tsohon shugaba Donald Trump Amurka ta fara ayyana mayakan Houthi a matsayin 'yan ta'adda, duk da cewar a waccan lokaci kungiyoyin bayar da agaji da na kare hakkin dan Adam sun yi adawa da matakin.

A cikin watan Fabrairun shekarar 2021 ne kuma, shugaba Joe Biden ya janye mayakan na Houthi daga cikin 'Bakin Kundin' na 'yan ta'adda, a kokarinsa na neman sukaka samun damar shigar da kayayyakin agaji zuwa ga dubban mutanen da ke yankunan da yaki ya tagayyara in Yemen. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.