Ba a cimma matsaya ba kan tattaunawar kulla yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza
An gaza cimma matsaya game da tattaunawar da aka yi tsakanin Amurka da Qatar da Isra’ila da kuma Masar, kan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin da ake yi a Gaza, dai-dai lokacin da ake ta kiraye-kiraye ga Isra’ila ta takatar da shirinta na kai hari yankin Rafah.
Wallafawa ranar:
Kafin fara rikicin Hamas da Isra’ila, yankin na Rafah na da yawan mutane dubu dari 3, amma a sakamakon yadda mutane suka tsere daga gidajensu saboda hare-haren Isra’ila, a yanzu akwai sama da mutane miliyan daya da ke neman mafaka a cikinsa.
Isra’ila ta ce ta na kokarin kutsa kai yankin ne don kawar da mayakan Hamas da kuma kubutar da mutanenta da aka yi garkuwa da su.
Ta ce kafin ta kaddamar da hare-hare, akwai shirin da ta ke da shi na kwashe fararen hulan Falasdinawa daga yankin, sai dai hukumomin bada agaji sun ce babu wani shiri a kasa game da hakan, sannan babu wani wuri da masu gudun hijirar za su koma.
Babban jami’in bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffitha, ya ce hare-hare ta kasa da Isra’ila ke kai wa, ka iya dakatar da ayyukan jin kai.
"Ayyukan sojin Isra’ila a Rafah na iya haifar da asarar rayuka a Gaza, hakanan za su iya dakatar da ayyukan jin kai"
Hare-haren da Isra’ila ta fara kai wa yankin gabashin Rafah a cikin dare, ya haifar da firgici a tsakanin al’ummar yankin, lamarin da yasanya wa su fara fice wa daga cikinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu