Isa ga babban shafi

Akwai yiwuwar nasara a yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Zai yi wuya kungiyar Hamas ta yi watsi da tayin tsagaita wuta a Gaza daga masu shiga tsakani, sai dai kuma akwai yiwuwar ta kafe kai da fata kan cewa sai Isra’ila ta janye dakarun ta daga Gaza kafin duk wata tattaunawa.

Shugaban kungiyar Hamas Isma'il Haniyeh
Shugaban kungiyar Hamas Isma'il Haniyeh REUTERS - AZIZ TAHER
Talla

Masu shiga tsakani daga kasashen Qatar da Masar sun mikawa Hamas bukatar shiga yarjejeniyar tsagaita wuta kamar yadda Isra’ila da Amurka suka amince a wata ganawa ta birnin Paris.

 

Kawo yanzu dai jagororin kungiyar Hamas sun sanar da shirin bitar yarjejeniyar, kuma nan gaba kadan zasu sanar da matsayar su a kai.

 

Mahukuntan Falasdinu sun ce takardar yarjejeniyar tsagaita wutar ta birnin Paris, ta bukaci a dakatar da wuta a yakin da ake yi na tsahon kwana 40, sai dai bisa sharadin sakin duk Yahudawan da Hamas ta yi garkuwa da su fiye da 100.

 

Akwai kuma bukatar Hamas ta saki kafatanin sojojin Isra’ila da ta rike a matsayin fursunonin yaki, tare da mikawa mahukuntan Isra’ila gawarwakin mutanen da take rike da su.

 

Guda daga cikin kusoshin Falasdinu da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce yana da kwarin gwiwar cewa gwamnatin Hamas ba zata yi watsi da yarjejeniyar ba, amma dai akwai yiwuwar tu tirje wajen sakin mutanen da suka kama ko kuma dagewa wajen ganin an biya bukatun ta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.