Isa ga babban shafi

Isra'ila ta yi watsi da kudirin baiwa Falasdinu damar zama cikakkiyar kasa

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da kudirin da ke neman bai wa yankin Falasdinu damar zama kasa mai cin gashin kanta, wanda kasashe ke kallo a matsayin hanya daya tilo da za ta kawo karshen rikicin tsawon shekaru da bangarorin biyu suka shafe suna yi.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. via REUTERS - POOL
Talla

Netanyahu yayin jawabinsa gaban taron manema labarai, ya ce ya shaidawa babbar kawar Isra’ila Amurka cewa kasar na kalubalantar duk wani kudiri da zai baiwa yankin na Falsdinu damar zama kasa mai cin gashin kanta ko da bayan kawo karshen yakin da yanzu haka kasar ta Yahudu ke yi a Gaza.

A cewar Netanyahu, walau a yanzu ko a nan gaba, Isra’ila na bukatar cikakken iko ne da dukkanin wani yanki da ke yamma da Jordan domin rasa wannan dama za ta kalubalanci tsaro da karfin ikon Isra’ila a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Tuni dai fadar White House ta bakin sakataren tsaron Amurka John Kirby ta bayyana cewa ita kanta ta na kallon lamarin ta wata fuska daban.

Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da tsananta farmaki a yankin Gaza don kamala ceto ilahirin fursunonin Isra’ilan da Hamas ta kame tun ranar 7 ga watan Oktoba.

Zuwa yanzu Isra’ila ta kasha fararen hular da suka tasamma dubu 25 baya ga kame wasu fiye da dubu 6 da kuma raunata dubunnan daruruwa a hare-haren da ta ke kaiwa wanda wasu kasashen Duniya ke kallo a matsayin kisan kare dangi ga Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.