Isa ga babban shafi

Isra'ila ta kashe Falasdinawa dubu 24 cikin kwanaki 100 da fara luguden wuta a Gaza

Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare ta sama da kasa a sassan Gaza, inda a jiya Lahadi aka cika kwanaki 100 da fara yakin da ta kaddamar kan kungiyar Hamas a yankin na Falasdinawa, tashin hankalin da ke ci gaba da salwantar da rayukan dubban fararen hula, akasarinsu mata da kananan yara. 

Isra'ila na ci gaba da yiwa Falasdinawa kisan kare dangi.
Isra'ila na ci gaba da yiwa Falasdinawa kisan kare dangi. AP - Fatima Shbair
Talla

A baya bayan nan ne dai Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin cewar babu wanda ya isa ya dakatar da gwamnatinsa daga aniyar da ta kulla na kawo karshen kungiyar Hamas, duk da cewar gwamnatinsa na fuskantar karin matsin lamba daga hukumomin kasa da kasa saboda yawan fararen hular da ke rasa rayukansu a Gaza. 

Yanzu haka dai akwai fargabar yakin ka iya yaduwa zuwa wasu kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, musamman bayan jerin sabbin hare-haren da Amurka ta kai kan mayakan Houthi da Iran ke marawa baya ranar Asabar a Yemen, bayan da mayakan suka yi gargadin cewa akwai yiwuwar suka kai karin hare-hare kan jiragen ruwan da suke ratsa tekun maliya, muddin Isra’ila ba ta daina kisan kiyashin da take a Gaza ba. 

A can iyakar kasar ta Isra’ila ta Lebanon ma, abin ba sauki, inda ake ci gaba da musayar kai hare-haren makamai masu linzami tsakanin dakarunta da kungiyar Hezbollah, wadda ta rasa mayakan hudu, bayan da suka tsallaka cikin iyakar Isra’ila suka kuma budewa sojoji wuta. 

Sabbin alkaluman dai sun nuna cewar ya zuwa yanzu, Falasdinawa fiye da dubu 24 suka rasa rayukansu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Zirin Gaza, tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoban da ta gabata da mayakan Hamas suka kai mata tare da kashe kimanin mutane dubu 1 da 140.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.