Isa ga babban shafi
YAKIN UKRAINE-IZRAELA

Biden ya zargi yan majalisar dattawan Republican da kokarin durkusar da Ukraine a fagen daga

Bayan da yan majalisar dattawan Republican su ka haifar da tarnaki ga shirinsa na tallafawa kasashen Ukraine da Israela da  biliyoyin dalar amurka a jiya laraba, shugaban Amurka Joe Biden ya dangatan matakanin da zama mai cike da hadari da  tada hankali sosai. Sai dai kuma ya bayyana cewa,  a shirye yake ya yi sassauto  dangane da  abin da ya shafi  da samar da sauki ga siyasar da ta shafi kan iyakokin kasar ta Amuruka.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden
Shugaban kasar Amurka Joe Biden © Jonathan Ernst / AP
Talla

Shugaban na Amuruka Joe Biden ya yi kashedin irin mummunan koma bayan da ya ce, za a girba a karkashin wannan mataki, da ya bayyana, a matsayin babbar kyauta ko garabasa ga shugaba Vladimir Poutine na Rasha, a karkashin wannan  mataki da majalisar dattawan ta dauka, na hana Amurka ta tallafa  da kudaden yaki da yawansu ya kai dalar biliyan  110 ga kasshen Ukraine da Israël,  da kuma kula da wasu muradu da suka shafi tsaron kasar ta Amurka.

’Yan awowi bayan gargadi ne, ’yan majalisar dattawan  republicans, su ka kada kuri’ar watsi da shirin na Biden, kamar yadda suka sha yin barazanar aiwatarwa a duk tsawon mako.

A lokacin da yake bayyana takaicinsa kan wannan koma baya, shugaba Biden, ya ce, yan majalisar na Republican a shirye suke,  su durkusar da Ukraine kan guiwowinta  a fagen daga, da kuma haifar da barazana ga yanayin tsaron kasar ta Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.