Shugaban Amurka Joe Biden, ya bayyana aniyar hana yahudawan dake cin zarafin Falastinawa Visa
Daukar matakin dai na Amurka na zama irinsa na farko da Amurka ta gabatar da barazanr amfani da matakan ladaftar kan yahudawan yan kakagidan. Kamar yadda shugaban na Amuruka Joe Biden ya sanar a cikin wani rubutu a shafin jaridar Washington Post.
Wallafawa ranar:
Wakilin Radio France Internationale RFI a Miami, David Thomson.Ya ce, shugaban Amuruka ya bukaci mahukumtan isaraela da cewa, su yi duk yadda ya dace wajen kawar dabi’ar cin zarafin falestinawa, ko kuma sabanin hakan, Amurka a shirye take ta dau wasu jerin matakan ladaftarwa, da suka shafi hana bada Visar shiga kasarta ga masu tsatsauran raáyin yahudawan, da ke cin zarafin falestinawa daga mako mai zuwa.
wannan baraza ta Amuruka na nuna yadda Amuruka ta fara kallon rikicin na Israela da Falestinawa da idonu irin na adalci, domin samo hanyoyin kawo karshen mummunar kiyayyar dake tsakaninsu. hakan kuma na nuna cewa, duk da Amurka bata fito fili ta bayyana Izraela a matsayin mai laifi ba, amma ta labe wajen dorawa daidaikun yahudawa yan kakagida laifin cin zarafin Falestinawa, abinda ke nuna cewa, Amurka ta zama tabarmar mai nade tabarmar kumya da hauka ne
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu