Henry Kissinger, jami'in diflomasiyyar Amurka ya mutu yana da shekaru 100
Henry Kissinger, jami'in diflomasiyyar Amurka mai kishin kasa, wanda ya taimaka ta fuskar kare martabar Amurka da kuma taimaka wajen daidaita duniya bayan yakin duniya na biyu, ya mutu ranar Laraba, ya na mai shekaru 100.
Wallafawa ranar:
Kissinger,ya mutu a gidansa da ke Connecticut, labarin da kamfaninsa mai suna Kissinger Associates ya sanar ,za a gudanar da jana'izar sa cikin sirri tare da wani taron tunawa da za a yi a baya a New York, inda Kissinger ya girma bayan danginsa Bayahude sun gudu daga Jamus na Nazi.
Sanarwar ba ta bayar da dalilin mutuwar ba. Kissinger ya kasance mai himma tun yana dan shekara dari, inda ya je kasar China a watan Yuli don ganawa da shugaba Xi Jinping.
Kasar China ta kasance daya daga cikin mafi dawwamammen abubuwan gado na Kissinger.
Tarihi ya nuna cewa a lokaci cacar-baka da Tarayyar Soviet, Kissinger ya isa birnin Beijing a asirce, inda ya kai ziyara mai tarihi a shekarar 1972 da shugaban kasar Richard Nixon ya kai, daga baya kuma Amurka ta kulla alaka da wannan kasa.
Kissinger na daya daga cikin mutanen da aka raina a yawancin kasashen duniya, ma'aikatar harkokin wajen kasar China a ranar Alhamis ta bayyana marigayi jami'in diflomasiyyar Amurka a matsayin "tsoho kuma aminin jama'ar China."
Kissinger ya dade yana nuna damuwa da goyon bayan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin China da Amurka, yana ziyartar kasar China fiye da sau dari, tare da ba da gudummawar tarihi don inganta dangantakar dake tsakanin China da Amurka," in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin.
Fumio Kishida, Firaministan kasar Japan da ke kawance da Amurka, ya yabawa Kissinger saboda "gaggarumar gudumawar da ya bayar" wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Asiya, "ciki har da daidaita huldar diflomasiyya tsakanin Amurka da China."
"Amurka ta rasa daya daga cikin masu dogaro da kai da kuma bayyana ra'ayoyinsu kan harkokin kasashen waje sakamakon rasuwar Henry Kissinger," in ji tsohon shugaban kasar George W. Bush dan jam'iyyar Republican a cikin wata sanarwa.
An bai wa Kissinger lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel kan shawarwarin kawo karshen yakin Vietnam, duk da cewa rikicin bai kare ba nan take kuma takwaransa na Arewacin Vietnam, Le Duc Tho, ya ki karbar kyautar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu