Isa ga babban shafi

Jinkiri wajen amincewa da kudaden tallafin yakin Ukraine murkushe Kiev ne-Amurka

Fadar gwamnatin Amurka ta White House, ta gargadi majalisar kasar game da jinkiri wajen amincewa da kudaden tallafawa yakin Ukraine da cewa tamakar wani mataki ne murkushe Kiev a fagen daga.

Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky.
Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky. AP - Evan Vucci
Talla

Yayin da Majalisar Amurka ke ci gaba da jan kafa wajen amincewa da kunshin tallafawa Ukraine da shugaba Joe Biden ya gabatar, Daraktar Kasafin Kudi Shalanda Young ta aike da wasikan gargadin, inda acikinta take cewa lokaci na neman kurewa Amurka na biyan wadannnan bukatu, wanda sabaninsa hadari ne ga tsaron kasar.

Jami’ar ta ce muddun ba a kai ga cimma wata yarjejeniya da Majalisa ba har zuwa karshen wannan shekara, domin samun kudaden sayo wa Ukraine karin makamai da kayan aiki da kuma samar wa su kansu sojojin Amurka kayan aiki, tamkar ankai kasar filin daga ne an barota, domin babu wata hanyar siddabaru ta samun kudi.

Duk da cewa gwamnatin Amurka ta dauki tsawon watanni ta na kokarin neman karin taimako ga kasar Ukraine da yaki ya daidaita, wasikar ta ranar Litinin ta nuna tsananin bukatar gaggawa kan yakin da shugaba Joe Biden ya bayyana a matsayin mai mutukar muhimminci ga makomar dimokuradiyyar duniya.

Cikin wasikar da Young ta aikawa shugabannin majalisar dokokin Amurka, ta jaddada hadarin da ke tattare da rashin amincewa da samun kudaden, inda ta ce tamkar bai wa sojojin Rasha damar samun nasara ce a yakin, kuma ci gaba da tallafawa Ukraine shi ne matsayin kokari na kaucewa fadada rikici a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.