Isa ga babban shafi

Amurka za ta bai wa Ukraine karin tallafin yaki da Rasha

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya kai ziyarar ba-zata zuwa Ukraine a wannan Laraba, inda ake sa ran  zai  shafe kwanaki biyu, wadanda a cikinsu zai sanar da mika wa kasar karin kunshin tallafi don taimaka wa  fafutukar da take yi kan dakile mamayar da sojojin Rasha ke yi mata. 

Anthony Blinken tare da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky
Anthony Blinken tare da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky via REUTERS - POOL
Talla

 

Karo na hudu kenan da Blinken ke ziyartar Ukraine tun bayan da Rasha ta kaddamar da yaki kanta a watan Fabarairun shekarar 2022. 

Sakataren Harkokin Wajen na Amurka ya sauka a Ukraine din ne sa’o’i kalilan bayan harin da Rasha  ta kai  kan Kyiv babban birnin kasar, kodayake babu rahoton hasarar rai ko na dukiya. 

Cikin kwanaki biyun da zai shafe yana ziyarar, ana sa ran Blinken ya sanar da karin tallafin kayan yaki na sama da dala biliyan 1 da Amurka za ta bai wa Ukraine. 

Yunkurin na Amurka ya zo ne bayan da a baya-bayan nan wasu kafafen yada labarai suka ruwaito wasu jami’an Amurka da ba su bayyana sunyensu ba na cewa, hare-haren da sojojin Ukraine suka kaddamar da zummar kwato yankunansu da Rasha ta mamaye na tattare da rauni, tare da fuskantar rashin dabarun yaki, caccakar da ta fusata jami’an Ukraine. 

Ya zuwa yanzu dakarun Ukraine sun yi nasarar kwato kauyuka da wasu kananan yankuna fiye da 12 daga hannun sojojin Rasha, sai dai sun gaza kutsawa zuwa sauran manyan yankunan da suke hankoron sake kwatowa saboda dalilai na nakiyoyin da aka dasa a hanyoyi da kuma ramukan gwalalon da aka aka haka. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.