Isa ga babban shafi

Kawayen Amurka sun juya baya ga shirin bai wa Ukraine bama-bamai masu kwanso

Kaso mai yawa na manyan kawayen Amurka sun soki matakinta na aikewa Ukraine nau’ikan bama-bamai masu kwanso da aka fi sani da Cluster wanda kasar ta sanar da bayarwa a juma’ar da ta gabata, bayan da shugaba Joe Biden ya bayyana cewa mataki ne mai matukar wahala gabanin amincewa da shi.

Nau'ikan bama-bamai masu kwanso na Cluster da Amurka ke shirin baiwa Ukraine.
Nau'ikan bama-bamai masu kwanso na Cluster da Amurka ke shirin baiwa Ukraine. AFP - MIKE NELSON
Talla

Bayan sanar da matakin a juma’ar da ta gabata, tsakanin jiya asabar da yau lahadi kasashen Birtaniya Canada da kuma New Zealand baya ga Spain sun nuna rashin goyon bayansu ga shirin baiwa Ukraine bama-baman wanda tsawon shekaru kasashe fiya da 100 suka sanya hannu kan haramta amfani da shi saboda hadarinsa ga bil’adama.

Nau’ikan bama-baman wanda duk guda daya kan iya tarwatsa kwatankwacin filin kwallo 3, na dauke da ‘ya’ya ne ta yadda yak e iya ci gaba da tasiri akalla shekaru 10 bayan amfani da shi a waje.

Tuni dai Ukraine ta sha alwashin cewa ba ta shirin amfani da nau’in bom din wajen kai hari kan abokiyar fadanta Rasha, sai dai duk da hakan kasashe na ci gaba da gargadi game da matakin na Amurka.

Tun a yammacin jiya asabar Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya nanata batun cewa sam kasarsa ba za ta goyi bayan kai nau’ikan bama-baman Ukraine ba.

Bayanai sun nuna cewa Amurka ta taba amfani da nau'in bama-baman masu kwanso kan Iraqi kuma tun daga wancan lokaci ne kasashe suka yi tarayya wajen haramta amfani da shi saboda hadarinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.