Za a takaita zirga zirgar ababan hawa a birnin Paris
FARANSA – Hukumomin dake shirya gasar Olympics da za'ayi a birnin Paris ta kasar Faransa a shekara mai zuwa, sun sanar da cewar za'a takaita zirga zirgar ababan hawa a sassan birnin da dama saboda yawan jama'ar da ake saran su halarci wasannin.
Wallafawa ranar:
Shugaban 'yan sandan da zasu sanya ido wajen tabbatar da tsaro, Laurent Nunez yace masu dauke da tikiti ne kawai za'a bai wa damar shiga filayen wasanni, yayin da aka saka shingen da zai kare 'yan kallo da masu wasa.
Jami'in yace za'a hana zirga zirga a wurare da dama na birnin Paris da za'a gudanar da wadannan wasanni daban daban a yammaci da kuma tsakiyar birnin Paris.
Daga cikin yankunan da za'a hana zirga zirga gaba daya, akwai Place la Concorde dake tsakiyar Paris, inda za'a gudanar da wasan kwallon kwando da kuma rawar 'break dancing', sai kuma Trocadero da tsaunin Eiffel Tower da Champ-de-Mars.
Sai dai sanarwar tace za'a a bar masu amfani da kekuna su shiga inda suke so.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu