Isa ga babban shafi

An gano yadda na'urar VAR ke barna fiye da gyara- Bincike

Masu ruwa da tsaki na ci gaba da mika korafe-korafe game da kuskuren da na’urar taimakawa alkalin wasa ta VAR ke ci gaba da tafkawa a wasannin gasar Firimiyar Ingila, ta yadda na'urar ke sahale bugun fenariti a wajen da bai kamata ba, baya ga soke kwallayen da suka cancanta.

Alkalin wasa Wilmar Roldan yayin nazartar na'urar VAR taimaka wa alkalin wasa da maimaicin hoton bidiyon da ta nada.
Alkalin wasa Wilmar Roldan yayin nazartar na'urar VAR taimaka wa alkalin wasa da maimaicin hoton bidiyon da ta nada. Pool via REUTERS - RODRIGO BUENDIA
Talla

Lamarin da ya faru a wasan da Fulham ta yi nasara kan Wolverhampton Wanderes da kwallaye 3 da 2 jiya Litinin karkashin gasar ta Firimiyar ya ja hankalin masharhanta bayan da alkalin wasa Michael Salisbury ya amince da bugun fenariti ga Fulham a wajen da kowanne bangare ya yi ittifakin babu bugun.

Wasu alkaluma da aka tattara sun nuna yadda VAR ke tafka manyan kurakurai a cikin wannan kaka kwatankwacin kakar wasan da ta gabata lamarin da ya sanya masu sharhi ke ganin na’urar ta haddasa matsaloli fiye da gyaran da ta yi daga lokacin da aka faro amfani da ita shekaru 4 da suka gabata zuwa yanzu.

A wannan kaka, tun gabanin kukuren na wasan Wolves da Fulham, kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ke matsayin kungiyar da VAR ta fara yi wa barna bayan soke kwallon Luis Dias yayin wasansu da Brighton duk kuwa da yadda su kansu jami’an da ke kula da na’urar Darren da Dan Cook suka yi imanin cewa kwallon ta cancanta, amma na’urar ta nunawa alkalin wasa cewa babu kwallo kuma nan take ya soke ta dalilin da ya sanya aka tashi wasa Brighton na da 2 Liverpool na da 1 gabanin bai wa tawagar ta Jurgen Klopp hakura game da hukuncin daga bisani.

A bangare guda akwai kuma haduwar Fulham da West Ham wanda aka tashi wasa babu kwallo, shima dai a wannan wasa na ranar 6 ga watan Fabarairun 2021 anga tarin kurakuren da VAR ta tafka, bayan korar ‘yan wasa har biyu ba tare da hakkinsu ba da kuma soke kwallo guda.

A ranar 8 ga watan Aprilun da ya gabata ma yayin wasan da Totttenham ta yi nasara kan Brighton da kwallaye 2 da 1, VAR ta ki amincewa da bai wa Brighton bugun fenariti duk kuwa yadda aka tatsile Kaoru Mitoma a da’irar 18, haka zalika daga bisani na’urar ta soke kwallayen kungiyar har guda biyu.

Sauran kura-kuran na VAR sun hada da na wasan canjaras din Arsenal da Brentford wanda aka sokewa Arsenal din kwallo, gabanin bai wa kungiyar hakuri bayan wasa, wanda ake ganin shi ya ragewa kungiyar karsashi tare da mako ta daga saman teburin Firimiya a kakar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.