Isa ga babban shafi

Ronaldo ya ki karbar bugun fenariti a wasan Al Nassr da Persepolis ta Iran

Tauraron Al Nassr ta Saudiya, Cristiano Ronaldo ya ki amincewa da karbar bugun fenaritin da alkalin wasa ya bashi a wasansu na daren jiya litinin, bayan da ya fadi a gab da da’irar 18, duk kuwa da yadda ake kallon dan wasan a sahun masu neman bugun na fenariti da gan-gan.

Cristiano Ronaldo a filin wasan birnin Riyadh.
Cristiano Ronaldo a filin wasan birnin Riyadh. REUTERS - AHMED YOSRI
Talla

Wannan lamari dai ya faru ne a wasan cin kofin nahiyar Asia a matakin rukuni da aka doka cikin daren jiya tsakanin Al Nassr ta Saudiyan da Persepolis ta Iran, wasan da aka tashi babu kwallo tsakanin kungiyoyin biyu.

A minti na biyu na fara wasa ne, mai tsaron baya na Persepolis ya hankade Ronaldo inda nan ta ke alkalin wasa Ma Ning dan China ya bayar da bugun fenariti amma kuma Ronaldon ya yi masa bayanin cewa babu fenariti a wajen.

Bayan da alkalin wasan ya duba na’ura ne kuma ya tabbatar da cewa babu bugun fenariti a wajen lamarin da ya tseratar da Persepolis wadda ke matsayin ta 2 a rukuninsu na E.

An dai kamala wasan na jiya babu kwallo duk da yadda aka kori Ali Lajami daga fili tun a minti na 17 da fara wasa.

Al Nassr wadda ke jagorancin rukuninta na E tuni ta samu cancantar kai wa mataki na gaba tun kafin wasan na jiya a Riyadh inda ta ke da maki 13 tazarar maki 5 tsakaninta da Persepolis da ke matsayin ta 3, kuma daga wannan wasa ta kammala wasanninta na rukuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.