Isa ga babban shafi

Cristiano Ronaldo ya sake kafa sabon tarihi a duniyar tamola

Kyaftin din Portugal Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin zama dan wasa na farko da ya doka wasannin kasa da kasa 200 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2024 da suka doke Iceland da ci 1-0.

Kaftin Portugal Cristiano Ronaldo yayin murnar zura kwallo a wasan neman gurbi a gasar Euro 2024 da kasarsa ta doke Iceland da 1-0, a daren Talata 20/06/23.
Kaftin Portugal Cristiano Ronaldo yayin murnar zura kwallo a wasan neman gurbi a gasar Euro 2024 da kasarsa ta doke Iceland da 1-0, a daren Talata 20/06/23. AP - Árni Torfason
Talla

Dan wasan mai shekaru 38 shine ya ci kwallon da ta bai wa Purtgal nasara a mintuna na 89 ana daf da karkare wasa.

Da farko alkali ya zaci kwallon satar fage ce, amma na’urar VAR ya amince da cin lamarin da ya farantawa Ronaldo a daren mai cike da tarihi.

Kaftin Portugal Cristiano Ronaldo yayin wasan neman gurbi a gasar Euro 2024 da kasarsa ta doke Iceland da 1-0, a daren Talata 20/06/23.
Kaftin Portugal Cristiano Ronaldo yayin wasan neman gurbi a gasar Euro 2024 da kasarsa ta doke Iceland da 1-0, a daren Talata 20/06/23. AP - Brynjar Gunnarsson

Wannan ita ce kwallonsa na 123 da Ronaldo ya ci a duniya, wanda ya kara masa tarihin yawan kwallaye a duniya.

Sabon tarihi

Ronaldo na Al-Nassr ya karya tarihin dan wasan Kuwait Bader Al-Mutawa da cika wasanni 196 a cikin watan Maris din da ya gabata – kuma tuni Guinness World Records suka mika masa shaidar yabo tun kafin fara wasa.

Kaftin Portugal Cristiano Ronaldo lokacin da ya karbi shaidar tarihin doka wasar kasa da kasa 200 gabinin a wasan neman gurbi a gasar Euro 2024 da kasarsa ta doke Iceland da 1-0, a daren Talata 20/06/23.
Kaftin Portugal Cristiano Ronaldo lokacin da ya karbi shaidar tarihin doka wasar kasa da kasa 200 gabinin a wasan neman gurbi a gasar Euro 2024 da kasarsa ta doke Iceland da 1-0, a daren Talata 20/06/23. AP - Brynjar Gunnarsson

Ronaldo ya cika shekaru 20 da soma bugawa kasarsaPortugal wasa, bayan ya fara a shekarar 2003, kuma har yanzu yana taka leda a kungiyar duk da cewa ya bar Turai zuwa Saudiyya bayan kammala gasar cin kofin duniya.

Ballon d'Or

Tsohon dan wasan Sporting Lisbon, Manchester United, Real Madrid da Juventus ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar.

Kwallon da ya ci ta biyar a wasan neman tikitin shiga gasar Euro 2024 ya taimaka wa Portugal da ci hudu a wasanni hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.