Isa ga babban shafi

Sujjadar Ronaldo bayan nasarar zura kwallo ta janyo cece-kuce

Sujjadar Cristiano Ronaldo bayan zura kwallo a wasansu na jiya talata wanda Al Nassr ta yi nasara kan Al-Shabaab da kwallaye 3 da 2 ya janyo cece-kuce a duniyar magoya bayan kwallo, lura da yadda tauraron ya yi salón murnar da ba a taba ganin wani wanda ba musulmi ba ya yi irinta walau bayan nasarar zura kwallo ko don wata murna daban.

Cristiano Ronaldo yayin sujjada bayan nasarar zura kwallo a wasansu na jiya tare da Ittihad.
Cristiano Ronaldo yayin sujjada bayan nasarar zura kwallo a wasansu na jiya tare da Ittihad. © Al Nassr
Talla

Salon murnar kwallon na Ronaldo dai ya kayatar da dimbin magoya bayansa musamman a cikin kasar ta Saudi  Arabia da ya koma takawa leda a farkon shekarar nan bayan rabuwa da Manchester United.

Yayin wasan na jiya dai, Al Shabaab ta fara zura kwallaye 2 a ragar Al Nassr gabanin kwallon Talisca da Ghareeb yayinda bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma Ronaldon ya zura kwallon ta 3 wadda ke nuna tabbacin ci gaban fatan Al Nassr na yiwuwar iya lashe kofin gasar bayan rage tazarar da ke tsakaninta da Al Ittihad zuwa maki 3 cal kungiyar da yanzu haka ke saman teburin gasar ta Saudi Lig dai dai lokacin da ya rage wasanni 2 a kammala kakar bana.

Wasu faifan bidiyo dai sun nuna yadda dan wasan mai shekaru 38 bayan zura kwallon kamar yadda ya saba ya yi fitaccen salón murnar da aka fi sanin shi da ita wato SIUU sannan ya kara da sujjada lamarin da ya sanya ilahirin filin wasan karadewa da kabbara hade da sowa.

Wannan murna ta Ronaldo dai ta zamo babban batun tattaunawa tare da tafka muhawara a dandalin sada zumunta tsakanin magoya baya, yayinda kafafen labaran wasanni da dama suka kawar da kai.

Idan har Al Nassr ta iya nasarar doke Ettifaq a asabar mai zuwa kai tsaye kungiyar ta koma maki kankankan da Al Ittihad tare da tunkarar lashe kofin na Saudi Lig karo na 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.