Isa ga babban shafi
CIN KOFIN TURAI

Arsenal ta ragargaji Lens da ci 6-0 a gasar zakarun Turai

Duniya – Kungiyar kwallon kafar Arsenal ta ragargaji Lens ta Faransa da ci 6 - 0 a karawar da suka yi na cin kofin zakarun nahiyar Turai a daren jiya, nasarar da ya jaddada jagorancinta a teburin gasar.

'Dan wasan Arsenal Kai Havertz ke murnar kwallon da ya jefa daren jiya
'Dan wasan Arsenal Kai Havertz ke murnar kwallon da ya jefa daren jiya AFP - IAN KINGTON
Talla

Wannan nasara ta dada tabbatar da fatar da magoya bayan kungiyar ke da ita na farfadowar kungiyar ta su a cikin wannan gasa, bayan kwashe shekaru 5 ba tare da an dama da su ba.

Zaratan 'yan wasa irinsu Kai Haverts da Gabriel Jesus da Bukayo Saka da Gabriel Martinelli da Martin Odegard da kuma Jorginho suka zazzagawa Lens wadannan kwallaye guda 6.

Nasarar ta sanya Arsenal nan take ta samu damar zuwa zagaye na 2, wato zagayen 'yan 16 da maki 12 a matsayin farko na rukunin B, yayin da PSV ke matsayi na 2 da maki 8, sai kuma Lens da maki 5, sannan Seveilla da maki 2 a matakin karshe.

Arsenal wadda ke kokarin sake gina sabuwar kungiya a karkashin jagorancin Mikel Arteta, na taka rawar gani a gasar Firimiya, wadda yanzu haka take jagoranci da maki 30 a gaban kungiyar Manchester City mai rike da kofi, wadda ke da maki 29.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.