Isa ga babban shafi

'Dan wasan Ghana ya mutu bayan faduwar da ya yi a filin kwallo

Turai – Wani ‘dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafar Ghana, Rapahel Dwamena ya mutu jiya asabar, bayan ya yanke jiki ya fadi lokacin da kungiyarsa ta KF Egnatia ke karawa da FK Partizani agasar lig na kasar Albania.

Marigayi Raphael Dwamenalokacin da yake yiwa Ghana wasa a gasar cin kofin Afirka
Marigayi Raphael Dwamenalokacin da yake yiwa Ghana wasa a gasar cin kofin Afirka AFP - YASUYOSHI CHIBA
Talla

Hukumar kwallon kafar kasar tace ma’aikatan kula da lafiya sun ruga domin kai masa dauki lokacin da ya gamu da hadarin, amma daga bisani sai ya rasu a asibiti yana da shekaru 28.

Dwamena ya bugawa babbar kungiyar kwallon kafar Ghana ta Black Stars was an kwallo har sau 8, kuma an taba bayyana shi a matsayin daya daga cikin taurarun ‘yan wasan kasar, amma sai ya gamu da cutar bugun zuciya yayin wasannin da yake yi abinda ya dakushe kimarsa.

A shekarar 2017 wannan matsala ta bugun zuciya ta hana shi sauya sheka zuwa kungiyar Brighton dake Ingila, amma daga baya ya koma kasar Spain.

Shekaru 4 bayan haka, Dwamena ya yanke jiki ya fadi lokacin da yake wasa a Austria tsakanin kungiyar Blau-Weiss Linz da Hertberg, amma kuma sai ya samu lafiya daga baya, matakin da ya bashi damar komawa ci gaba da wasannin sa.

Kafin wannan hadarin, an yiwa Dwamena aiki a zuciyarsa a shekarar 2020 tare da yi masa dashen wata na’ura a kirjinsa da zata dinga taimaka masa wajen kare lafiyarsa lokacin wasanni.

Bayan dashen, ‘dan wasan ya ci gaba da sana’arsa a kasashen Denmark da Austria da kuma Switzerland kafin ya koma kungiyar KF Egnatia ta Albania a watan Janairun wannan shekara.

Marigayin ne ke sahun gaba wajen jefa kwallaye a mafi yawa a raga a kakar bana, saboda kwallaye 9 da ya jefa kafin mutuwarsa.

Kungiyar FC Zurich ta Switzerland tabi sahun masu juyayin mutuwar Dwamena wajen wallafa hotansa a shafinta na yanar gizo, inda ta bayyana cewar ba zata taba mantawa da gudumawar da ya bayar ba.

Sakamakon mutuwar Dwamena, hukumar kwallon kafar Albania ta soke daukacin wasannin da aka shirya yi a karshen wannan mako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.