Isa ga babban shafi

Magoya bayan Manchester United na shirya zanga zangar lumana

Turai – Magoya bayan Manchester United na shirya zanga zangar lumana a karshen mako mai zuwa, lokacin da kungiyar za ta kara da Luton Town a gasar Firimiya, domin nuna bacin ransu da irin koma bayan da kungiyar ke samu a karkashin jagorancin iyalan gidan Glazer.

Filin wasan Manchester United na Old Trafford
Filin wasan Manchester United na Old Trafford © AFP / OLI SCARFF
Talla

Magoya bayan na bukatar ganin an kammala sayar da kungiyar ce domin baiwa masu sha’awar zuba jari karbar ta da kuma zuba makudan kudade don tada komadarta da zummar ganin ta dawo da karsashin da aka santa da shi na gogayya a tsakaninta da manyan kungiyoyin dake Turai.

Marcus Rashford, daya daga cikin taurarun Manchester United
Marcus Rashford, daya daga cikin taurarun Manchester United AP - Dave Thompson

Masu goyan bayan kungiyar sun yi kira ga jama’a da su taru a bangaren arewa maso yamma na filin wasan kungiyar ta su dake birnin Manchester, domin gudanar da zanga zangar da suka ce ta lumana ce.

Wannan ne zai zama zanga zangar farko tun bayan da ya bayyana cewar wani attajiri Sir Jim Ratchliffe na bukatar sayen hannun jari mara rinjaye a kungiyar, matakin da ba zai sauya mallakar jari mafi yawa dake hannun iyalan Glazer ba.

Ana saran Ratchliff ya zuba kudin da ya kai Fam miliyan 254 wajen inganta filin wasan Old Trafford.

Yanzu haka kungiyar Manchester United ta barar da wasannin ta guda 9, daga cikin 17 da ta buga a wannan kakar, abinda ke barazana a kan makomar ta na zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Tun bayan murabus din Sir Alex Ferguson daga jagorancin kungiyar a shekarar 2013, sau 4 kawai Manchester United ta kai zagayen ‘yan 16 na gasar cin kofin zakarun Turai.

Ko a jiya kungiyar ta sha kashi a hannun kungiyar FC Copenhagen da ci 4 da 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.