Isa ga babban shafi

Diaz ya roki masu garkuwa da mahaifinsa su sako shi

Dan wasan gaba Liverpool dan asalin Colombia Luis Diaz, ya roki wadanda suka yi garkuwa da mahaifinsa su gaggauta sakoshi don kawo karshen dakon dawowarsa da suke yi.

Luis Diaz après son but contre Luton, le 5 novembre 2023.
Luis Diaz après son but contre Luton, le 5 novembre 2023. REUTERS - IAN WALTON
Talla

A ranar 28 ga watan daya gaba ne aka yi garkuwa da mahaifan dan wasan, bayan da aka yi musu barazana da bindiga a garinsu Barracncas, sai dai tuni aka gano mahaifiyarsa yayin da mahaifin ke hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

Bayan da ya rama Liverpool kwallo ana dab da tashi daga wasansu da Luton City, ya daga rigarsa da ke dauke da rubutun neman sakin mahaifinsa.

A cikin sanarwar da dan wasan ya fiyar bayan tashi daga wasan, ya ce sako mahaifinsa ne kadai zai kawo karshen kuncin da su ke ciki.

“Kowace dakika, ko wane miniti fargabarmu karuwa take yi, mahaifiyata da ‘yan uwana da ni kaina muna cikin damuwa, babu wata kalma da za ta iya kwatanta halin da muke ciki, kuma za a kawo karshen hakan ne idan ya dawo gida wajenmu”.

Diaz mai shekaru 26 ya kuma godewa al’ummar kasar Colombia da sauran kasashen duniya, bisa irin yadda suke jajanta musu kan wannan lamari da ya samesu.

Gwamnatin Colombia ta sanya kyauta ga duk wanda ya bada labarin inda Luis Manuel Diaz ya ke, tare da tura daruruwan jami’an soji da ‘yan sanda don kubutar da mahaifin dan wasan kwallon kafar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.