Isa ga babban shafi

'Yan tawayen ELN sun yi garkuwa da mahaifin dan wasan Liverpool a Colombia

Gwamnatin Colombia ta ce 'yan tawayen ELN sun yi garkuwa da mahaifin dan wasan Liverpool Luis Díaz. 

Mahaifiyar dan wasan Liverpool Luis Díaz na cikin 'yan Colombia da suka shiga zanga-zangar neman kubatar da mahaifin dan wasan daga hannun masu garkuwa.
Mahaifiyar dan wasan Liverpool Luis Díaz na cikin 'yan Colombia da suka shiga zanga-zangar neman kubatar da mahaifin dan wasan daga hannun masu garkuwa. AP - Leo Carrillo
Talla

Sanarwar gwamnati ta ce ’yan bindigar sun yi kokarin awon gaba da Luis Manuel Díaz da tare da mai dakinsa a ranar Asabar, amma da jami’an tsaro suka tinkare sai suka kyale mahaifiyar dan wasan a cikin mota, amma suka tsare da mahaifinsa. 

An tura daruruwan ‘yan sanda da sojoji domin kubutar da shi. 

Da farko dai 'yan sanda sun ce mai yiwuwa ayyukan gungun masu aikata laifuka ne, sai dai a ranar alhamis, wata tawagar gwamnati da a halin yanzu ke tattaunawa da kungiyar 'yan tawayen, ta ce tana da masaniya a hukumance cewa "wani bangare na ELN ne suka yi garkuwa da shi". 

Babbar kungiyar 'yan daba

ELN ita ce babbar ƙungiyar 'yan daba ta Colombia, kuma tun a shekarar 1964 take yaki da gwamnati kuma tana da mambobi kimanin 2,500. 

Sun fi tada kayar baya a yankin kan iyaka da Venezuela inda Luis Manuel Díaz da matarsa Cilenis Marulanda ke zaune. 

Yadda aka yi garkuwa da Manuel

Hotunan CCTV sun nuna yadda wasu mutane a kan babura ke bin motarsu da yammacin ranar Asabar. 

Inda suka cimmusu lokacin da suka tsaya a gidan mai a na Barrancas a lardin La Guajira da ke arewacin kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.