Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifan dan wasan Liverpool

Shugaban kasar Colombia Gustavo Petro, ya ce jami’an tsaro sun samu nasarar ceto mahaifiyar dan wasan gaba na kungiyar Liverpool Luiz Diaz daga hannun masu garkuwa da mutane, sai dai har yanzu ana kokarin kubutar da mahaifin dan wasan.

Dan wasan gaba na kungiyar Liverpool Luis Diaz.
Dan wasan gaba na kungiyar Liverpool Luis Diaz. REUTERS - MOLLY DARLINGTON
Talla

Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X, shugaba Petro ya ce an ceto mahaifiyar Diaz daga hannun miyagun ne a garin Barrancas da ke arewacin Colombia.

Bayanai sun ce mahaifan dan wasan na Liverpool sun shiga tashin hankali ne, bayan da gungun ‘yan bindiga haye kan babura suka yi awon gaba dasu daga wata tashar jirgin kasa.

Colombia na cikin kasashen kudancin Amurka da suke fama da barazanar kungiyoyin ‘yan tawaye da masu safarar miyagun kwayoyi, wadanda sau da dama kan yi garkuwa da mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.