Shirin "Duniyar Wasanni" na wannan makon yayi duba ne kan kyautar Ballan d’Or da aka bayar a makon da ya gabata, inda tauraron kwallon kafar Argentina da a yanzu ke kungiyar Inter Miami a Amurka, Lionel Messi, ya lashe kyautar gwarzon duniya ta Ballon d’Or karo na takwas. A wannan karon dai Erling Haaland ne ya zo na biyu sannan Kylian Mbappe ya zo na uku a bikin ba da kyautar ta Ballon d’Or.
Haka nan shirin ya tabo batun kwallon Zari Ruga da kasar Afrika ta Kudu ta lashe.
Wannan ne dai karo na farko da wata kasa ta taba lashe kofin a jere, bayan da zaratan ‘yan wasan na Afrka ta Kudu suka lallasa takwarorinsu na New Zealand da ci 12 da 11 a wasan karshen da aka yi a birin Paris na Faransa.
Ku danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu