Rike Real Madrid da Rayo Vallecano ta yi ya sakko da ita daga teburin La liga
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ta barar da damarmakin da ta samu a karawarta da Rayo Vallecano a filin wasa na Bernabeu, inda aka tashi babu ci a wasan.
Wallafawa ranar:
Da wannan sakamako, Madrid ta koma mataki na biyu a teburin gasar La liga, inda Girona da ta lallasa Osasuna da ci 4 da 2, ta dare kan teburin gasar.
Wannan ne dai karo na farko da kungiyar Vallecano ta samu maki daya a gidan Real Madrid tun shekarar 2000.
‘Yan wasan Carlo Ancelotti, sun kasa zura koda kwallo daya a damarmaki 22 da suka samu a wasan.
Tun kafin tafiya hutun rabin lokaci, an yi tunanin dan wasa Jude Bellingham ya samu rauni a kafatarsa, amma bayan duba shi da likitoci suka yi ya dawo inda ya ci gaba da wasa.
Mai horas da kungiyar Ancelotti ya ce a yau Litinin za a sake duba lafiyar dan wasan yadda ya kamata.
“Za a tuba Bellinham gobe, ba za mu yi sakaci mu dauka ba wani babban abu bane”.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu