Isa ga babban shafi

Rodrygo ya tsawaita kwantiraginsa da Madrid zuwa shekarar 2028

Dan wasan gaba na Real Madrid Rodrygo Goes ya tsawaita kwantiragi don ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2028, in ji kulob din na Spain cikin wata sanarwa ranar Alhamis. 

Dan wasan Madrid Rodrygo Goes yayin wasan La liga tsakaninsu da Sevilla.22/10/22
Dan wasan Madrid Rodrygo Goes yayin wasan La liga tsakaninsu da Sevilla.22/10/22 AP - Manu Fernandez
Talla

Dan wasan na Brazil ya amince ya tsawaita kwantiraginsa cikin mako daya da dan kasarsa Vinicius Junior da shi ma ya tsawaita zama a Santiago Bernabeu har zuwa shekarar 2027. 

Rodrygo, mai shekaru 22, ya yi kokarin tabuka abin azo agani a wannan kakar amma hakarsa bata cimma ruwa ba, amma dai Madrid na ji da shi sosai, inda ya ci kwallaye biyu a karawar da suka yi da Osasuna a watan Mayu, wajen taimakawa suka ya lashe kofin Copa del Rey na farko a Los Blancos tun shekarar 2014.

A shekarar 2018 dan wasan ya koma Madrid kan Yuro miliyan 45 daga Santos na Brazil, shekara guda tsakaninsa da Vinicius. 

Rodrygo ya zira kwallaye 39 a wasanni 179 da ya buga wa Marid a duk gasa, inda ya lashe kofunan La Liga biyu da gasar zakarun Turai a 2022. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.