Isa ga babban shafi

Brazil da Spain za su doka wasan sada zumunta don bai wa Vinicius hakuri

Brazil na shirin doka wani wasan sada zumunta da Spain a wani yunkuri na bayar da hakuri ga Vinicius Junior dama gangamin yaki da matsalar nuna wariya da ke kokarin rage farin jinin wasan na kwallon kafa.

Vinicius Junior na Brazil da ke taka leda da Real Madrid.
Vinicius Junior na Brazil da ke taka leda da Real Madrid. REUTERS - PABLO MORANO
Talla

Hukumar kwallon kafar Spain da ke sanar da shirin wasan sada zumuntar ta ce sun duba cikakken lokacin da ba zai cutar da kowanne bangare ba, wanda ke matsayin watan Maris na shekara mai zuwa don doka wasan.

Shugaban hukumar Luis Rubiales ya ce za a doka wasan ne da nufin nuna cikakken goyon baya ga Vinicius dama kungiyarsa ta Real Madrid baya ga kaddamar da gangamin yaki da nuna wariya a kasar wanda aka yiwa lakabi da ‘‘fata daya’’ da ake fatan ya dawo da karsashin ‘yan wasan da wannan matsala ta mayar da su koma baya.

Rubiales ya ce suna son nunawa duniya cewa babu hurumin nuna wariya a Spain, lura da yadda suka sanya hukuncin mai tsauri da kuma tara mai tarin yaw aga duk wanda aka samu da wannan dabi’a.

Duk dai wannan batu ya biyo bayan wariyar da Vinicius Junior ya fuskanta yayin wasan Real Madrid da Valencia a watan Mayu lokacin da aka rika kiranshi da biri a cikin fili, cin mutuncin da ya ja hankalin duniyar kwallo.

Ko a asabar din da ta gabata Brazil ta doka wasa da Guinea a Barcelona yayinda za ta doka da Senegal cikin kwanaki 3 masu zuwa.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.