Isa ga babban shafi

Vinicius na ci gaba da samun goyon bayan masoya da abukan sana'arsa

'Yan wasa  da magoya bayan Real Madrid sun nuna goyon bayansu ga Vinicius Jr, a lokacin wasan da suka yi nasara kan Rayo Vallecano à Bernabeu da ci 2-1

Vinicius Jr na murna tare da abukan sana'arsa
Vinicius Jr na murna tare da abukan sana'arsa AP - Jose Breton
Talla

wannan dai, shine wasan Madrid na  farko tun bayan hari da kalaman kabilanci da aka kai kan dan wasan dan kasar Brazil, a wasansu da Valence, a ranar lahadin da ta gabata.

 Vinicius, zaune a gefe a runfar yan kwallo  sakamakon rashin saka shi a wasan da aka yi, sakamakon  raunin da ya samu.

Daukacin yan wasan kungiyoyin ne a tsakar fili sanye da fararen Jesi dake dauke da lamba 20. Lambar da Vinicius Jr, ke bugawa , a yayin da sukuma caftin din kungiyoyin suka daura wani kambi a damutsansu dake dauke da sakon kyamar kabilanci.

Su kuma  magoya bayan kuwa, mikewa suka yi ana minina 20 da soma buka wasan, gaba dayansu suka kira sunan Vinicius domin nuna goyon baya a gare shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.