Isa ga babban shafi

Liverpool ta samu nasarar farko cikin wasanni 5 a gasar Premier

Liverpool ta samu nasarar farko cikin wasanni 5 da ta buga a gasar Premier Ingila, bayan da ta lallasa Leeds United a gida da kwallaye 6-1.

'Yan wasan Liverpool yayin murnar samun nasarar lallasa Leeds United da kwallaye 6-1.
'Yan wasan Liverpool yayin murnar samun nasarar lallasa Leeds United da kwallaye 6-1. AP - Rui Vieira
Talla

Kungiyar ta samu gagarumar nasarar ce ta hannun ‘yan wasanta Muhd Salah da Diogo Jota wadanda dukkaninsu suka jefa kwallaye bibbiyu. Sai kuma Darwin Nunez dda Gakpo da suka jefa kwallo guda guda.

Rabon da Liverpool ta samu nasara a gasar Firimiya tun bayan lallasa Manchester United da ta yi da 7-0 a farkon watan Maris.

A halin yanzu Liverpool na matsayi na 8 a gasar Firimiyar Ingila da maki 47, maki daya tsakaninta da Brighton da ke matsayi na 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.