Isa ga babban shafi

Liverpool ka iya rasa tikitin gasar zakarun Turai bayan gaza nasara kan Chelsea

An tashi wasa babu kwallo tsakanin Liverpool da Chelsea a tattakin da tawagar ta Jurgen Klopp ta yi zuwa Stamford Bridge jiya talata, dai dai lokacin da kungiyoyin biyu dukkaninsu ke fuskantar koma baya a wannan kaka.

'Yan wasan Liverpool yayin haduwarsu da Chelsea a Stamford Bridge.
'Yan wasan Liverpool yayin haduwarsu da Chelsea a Stamford Bridge. AP - Frank Augstein
Talla

Chelsea dai ta doka wasan na jiya ba tare da Manaja ba, bayan sallamar kocinta Graham Potter a karshen mako, inda Bruno Saltor ya jagoranci wasan a matsayin manajan rikon kwarya.

Yayin wasan na jiya anga sauye sauye 6 da Jurgen Klopp ya yi a tawagar tasa wadda ta banbanta da wadda Manchester City ta yiwa dukan kawo wuka a karshen mako da kwallaye 4 da 1.

Chelsea dai ta samu damarmaki kan Liverpool amma kuma ta gaza kai labara a wasan na jiya, har da kwallon Mateo Kovacic da Ibrahima Konate ya barar da kuma kwallon Kai Havertz da Alisson Becker ya tare sai kuma kwallon Reece James da nau’rar VAR ta bayyana a ta satar fage.

Yayin wasan na jiya dai Jurgen Klopp bai yi amfani da ‘yan wasansa irin Mohamed Salah da Trent Alexander-Arnold da kuma Andy Robertson ba, haka zalika mai tsraon bayan kungiyar Virgil van Dijk wanda rashin lafiya ta hana shi haskawa a wasan na jiya.

Sakamakon wasan dai babban koma baya ne ga Liverpool da ke fatan karkare kakar bana a sahun ‘yan hudun saman teburin firimiya dai dai lokacin da yanzu haka ke matsayin ta 8 tazarar maki 7 tsakaninta da gurbin da ta ke hari inda Tottenham ta ke kuma ta ke da sauran wasanni 11.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.