Isa ga babban shafi
Liverpool-Mancity

Manchester City da Liverpool za su hadu a wasan gab da karshe na FA

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool za ta hadu da Manchester City a wasan gab da na karshe na cin kofin FA bayan nasararta ta lallasa Nottingham Forest a jiya lahadi da kwallo 1 mai ban haushi.

Haduwar Liverpool da Manchester City a ko da yaushe na kasancewa babban wasa.
Haduwar Liverpool da Manchester City a ko da yaushe na kasancewa babban wasa. POOL/AFP
Talla

Itama dai Manchester City ta yi nasara ne kan Southampton da kwallaye 4 da 1 wanda ya ba ta damar kai wa matakin wasan na gab da karshe.

A bangare guda Crystal Palace da ta yi nasara kan Everton da kwallaye 4 da nema za ta hadu da Chelsea wadda a asabar din da ta gabata ta lallasa Middlesbrough da kwallaye 2 da nema.

Liverpool wadda ta lashe kofin Carabao a wannan kaka na harin kofin na FA ne karo na 4 yayin da Manchester City jagorar firimiya ke harin kofin karo na 3.

Wasannin na gab da karshe dukkaninsu za su gudana ne a filin wasa na Wembley da ke London tsakanin ranakun 16 zuwa 17 ga watan Aprilu, wato kwanaki kalilan bayan Manchester City ta karbi bakoncin Liverpool a firimiyar ingila, kungiyoyin da suka juye zuwa manyan abokanan dabi a yanzu.

Kungiyoyin biyu da yanzu haka ke da tazarar maki 1 tal a tsakaninsu matsayin jagora da mai bi mata a teburin firimiya na tseren lashe kofuna 3 ne wannan kaka da suka kunshi na firimiyar da na zakarun Turai da kuma FA wanda kuma dukkaninsu za su iya bayar da mamaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.