Isa ga babban shafi

Liverpool ta kai zagayen 'yan 16 a gasar Turai duk da rashin abin kirki a Firimiya

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya bayyana matukar allfaharinsa bayan da suka yi nasarar tsallakawa zuwa zagayen kungiyoyi 16 a gasar zakarun nahiyar Turai.

Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah.
Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah. AP - Peter Byrne
Talla

Liverpool sun manta da mastalolin da suke samu a gasarsu ta cikin gida, wato Firimiyar Ingila, inda suka tsira daga rukuninsu na A, bayan doke Ajax da kwallaye 3 da nema lamarin da ya basu damar tsallakawa rukunin 'yan 16 na gasar.

Liverpool dai na bukatar canjaras ne don zuwa matakin yayin wasan na jiya amma sai kungiyar ta bayar da mamakin ratata kwallayen har 3 a ragar Ajax inda Mohamed Salah ya zura kwallon farko tun gabanin tafiya hutun rabin lokaci.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma Liverpool kara kwallaye 2 ta hannun 'yan wasanta Darwin Nunez da Harvey Elliott.

A cewar kocin na Liverpool, nasarorin da suke samu alamu na cewa za su kai labari a gasar ta cin kofin zakarun Turai.

Liverpool wadda ta kai wasan karshe a kakar da ta gabata gabanin rashin nasara a hannun Real Madrid yayin wasan karshe yanzu haka tana matsayin ta 8 a teburin firimiyar Ingila bayan da ta faro kakar bana da kafar hagu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.