Isa ga babban shafi

Faransawa 'yan jarida kusan 100 sun bukaci basu damar shiga Zirin Gaza

Faransawa ‘yan jarida kusan 100 sun sanya hannu kan wata takardar neman izinin a basu damar shiga Zirin Gaza domin yadawa duniya halin da yankin ke ciki, inda Isra’ila ke ci gaba da yi wa ruwan wuta sama, hare-haren da zuwa yanzu suka halaka Falasdinawa kusan dubu 10.

Wani dan jarida zaune da nau'rarsa ta daukar hoto a birnin Sderot na kudancin Isra'ila, yayin da yake kallon sararin samaniyar arewacin Zirin Gaza yayin da Isra'ila ta kai wani harin bam a ranar 18 ga Oktoba, 2023.
Wani dan jarida zaune da nau'rarsa ta daukar hoto a birnin Sderot na kudancin Isra'ila, yayin da yake kallon sararin samaniyar arewacin Zirin Gaza yayin da Isra'ila ta kai wani harin bam a ranar 18 ga Oktoba, 2023. © Jack Guez, AFP
Talla

Yayin kare matakin nasu, ‘yan jaridar sun ce duk cewa kafafen yada labarai na kasa da kasa na kokarta wa wajen yadawa duniya halin da ake ciki kan yakin Isra’ila da Hamas, kowa ya ga yadda ake samun banbancin samun cikakkun bayanai, yayin daukar rahoto daga cikin Isra’ila, yayin da hakan ba ya yiwuwa daga Zirin Gaza.

Tun bayan killacewar dolen da Isra’ila ta yi wa Zirin Gaza shekaru 16 da suka gabata, aka daina bai wa ‘yan Jarida damar shiga yankin, muddin gwamnatin kasar ta Isra’ila ba ta tantance su ba.

Wasu alkaluma da aka tattara a baya bayan nan sun nuna cewar, ‘yan jarida akalla 34 suka rasa rayukansu a hare-haren bam din da Isra’ila ke kai wa a Zirin Gaza, tun daga ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.