Isa ga babban shafi

Yaran da aka kashe a 2022 basu kai adadin da suka mutu a Gaza ba cikin mako 3

Kungiyar bayar agaji ta kasa da kasa ‘Save the Children’, ta ce adadin kananan yaran da suka mutu a Zirin Gaza sakamakon hare-haren Isra’ila, ya zarce yawan wadanda da aka rika kashewa a duk shekara yayin rikice-rikicen da aka rika yi a sassan duniya tun daga 2019.

Wasu yara Falasdinawa da suka jikkata a hare-haren da Isra'ila ta kai a kudancin Zirin Gaza. 17 ga Oktoban, 2023.
Wasu yara Falasdinawa da suka jikkata a hare-haren da Isra'ila ta kai a kudancin Zirin Gaza. 17 ga Oktoban, 2023. AFP - MAHMUD HAMS
Talla

Wani rahoto da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya  bayyana, ya nuna cewar yara 2,985 aka kashe a kasashe 24 cikin shekarar 2022, yayin da a 2021 aka kashe yara  2,515.

A shekara ta 2020 kuwa, rayukan kananan yaran 2,674 ne suka salwanta a cikin kasashe 22.

Sai dai a cikin rahoton da ta wallafa a ranar Lahadin da ta gabata, kungiyar da ke rajin kare yaran ta ‘Save the Children’ ta ce ya zuwa yanzu kananan yaran akalla 3,324 suka rasa rayukansu a Gaza, wasu 36 kuma a gabar  yammacin kogin Jordan, tun daga farkon watan Oktoba.

Wani batu da ke kara tayar da hankali a yankin Gaza kuma shi ne bacewar wasu yaran akalla 1,000, wadanda ake fargabar mai yiwuwa suna karkashin baraguzan gine-ginen da Isra’ila ta rusa yayin hare-haren da jiragen yakinta ke kaiwa.

A bangaren wadanda suka ji rauni kuwa, sabbin alkaluman jami’an lafiya sun nuna cewar, yara fiye da 6,000 ne suka jikkata a Gaza tun lokacin da Isra’ila ta kaddamar da hare-haren ramuwar gayya kan farmakin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda yayi sanadin kashe mutane sama da 1,400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.