Isa ga babban shafi

Ba haka kawai Hamas ta kai hari a Isra'ila ba - Guterres

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ba haka kawai kungiyar Hamas ta kaddamar da hare-hare kan Isra’ila ba, inda ya ce matakin da mayakan suka dauka, sakamako ne na yadda Isra’ilar ta shafe shekaru 56 tana gallaza wa Falasdinawa. 

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres. REUTERS - AMR ABDALLAH DALSH
Talla

Guterres ya bayyana haka ne yayin jawabi ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan halin da ake ciki a Gaza, inda ya ce Falasdinawa sun dade suna kallon yadda Isra’ila ke kwace musu yankuna, da rushe musu gidaje, yayin da a lokaci guda suke fama da tashe-tashen hankula, lamarin da ya tilasta musu debe tsammani daga samun nasarar warware matsalolin da suke ciki a siyasance. 

Sai dai Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya ce dukkanin korafe-korafen na Falasdinawa bai kamata su zama hujjar kaddamar da munanan hare-haren da Hamas ta yi ba, kazalika Isra’illa ba ta da hujjar ramuwar gayya kan wadanda ba su ji ba ba su gani ba a kan laifin da wasu tsiraru suka aikata. 

Jawabin na Antonio Guterres, ya sanya Ministan Harkokin Wajen Isra'ila ya soke ganawar da aka tsara za su yi da shi a wannan Talatar a birnin.

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a Gaza 

Dangane da adadin mutanen da suka mutu a Gaza kuwa sakamakon luguden wutar da jiragen Isra’ila ke yi, Ma'aikatar Lafiyar yankin na Falasdinu ta ce fararen hula 704 Isra'ila ta kashe cikin sa'o'i 24 da suka gabata. 

A jimlace Falasdinawa akalla 5,791 ne suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza, yayin da a bangarenta sama da mutane 1,400 suka mutu tun ranar 7 ga watan Oktoba. 

Macron ya kai ziyara Tel Avivi. 

Shugaban Faransa Macron, da ya kai ziyara a Tel Aviv, babban birnin Isra’illa kuwa, ya shawarci kawancen sojojin kasashen Yammacin Turai da ke yaki da ISIL da su mayar da hankalinsu kan murkushe Hamas.  

Macron ya kuma yi kira da a sake kaddamar da shirin zaman lafiyar yankin Falasdinu, ta hanyar ba su yancin zama kasa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.