Isa ga babban shafi

Kare rayuka da mutunta ayyukan jin kai a Gaza dole ne ba zabi ba - MDD

Shugaban hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Falasdinawa ‘yan gudun hijira, Philippe Lazzarini, ya ce kare rayuka da mutunta ayyukan jin kai a Gaza dole ne ba zabi ba.

Wani gini da jiragen yakin Isra'ila suka rusa a garin Khan Younis da ke Zirin Gaza. 17 Oktoba, 2023.
Wani gini da jiragen yakin Isra'ila suka rusa a garin Khan Younis da ke Zirin Gaza. 17 Oktoba, 2023. REUTERS - MOHAMMED SALEM
Talla

Kalaman babban jami’in dai martani ne ga Fira Ministan Isra’illa Benjamin Netanyahu, wanda a ranar Litinin yayi watsi da kiraye-kirayen tsgaita wuta tsakaninsa da Hamas a Zirin Gaza, kungiyar da ya sha alwashin ganin bayanta.

A cikin yankin na Gaza dai, kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent ta ce hare-haren Isra’ila ta sama da kasa a kusa da babban asibitin al-Quds, sun jefa jami’an lafiya gami da dubban Falasdinawa da ke gudun hijira cikin firgici.

Wannan na zuwa ne a yayin da ma’aikatar lafiyar yankin Gaza ta sanar da karuwar adadin Falasdinawan suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila zuwa mutane sama da dubu 8,300, cikinsu kuma har da kananan yara fiye da 3,450

Tuni dai jami’an Majalisar Dinkin Duniya suka bukaci Kwamitin Tsaro ya sake yunkurawa wajen ganin an tsagaita wuta a Zirin Gaza, a daidai lokacin da hukumar UNICEF ta yi gargadin cewa kananan yara sama da 450 ake kashewa ko kuma suke jikkata duk rana a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.