Harin Isra'ila ya kashe mutane sama da 100 a sansanin Jabaliyah
Rahotanni na nuna cewar, wani hari da sojojin Isra’ila suka kai sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliyah da ke Gaza, yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan dari.
Wallafawa ranar:
A yammacin Talatar nan ce dai sojojin Isra’ila suka kai kazamin harin, wanda ya lalata ilahirin gine-ginen da ke cikin sansanin.
Dr Mads Gilbert wani likita da ke goyon bayan Falasdinawa a yankin Gaza, ya ce jami’ansa sun tabbatar masa da mutumar kusan mutane dari yayin da wasu dari 3 suka jikkata, sanadiyar hare-haren da Isra’ila ta kai kan gidajen fararen hula 15 a sansanin Jabaliyah.
Gilbert ya ce man fetur ya fara kare a babban asibitin al-Shifa, wanda zai iya dakatar da aikin ceton rayukan jama’a.
Ya ce ya na mamakin jan kafar da shugaban Amurka Joe Biden da shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ke yi, wajen dakatar da wannan rikici da ke ci gaba da lakume rayukan dabasuji basu gani ba.
A nasa bangaren, shugaban wani asibitin Indonesia da ke yankin Gaza, ya ce har yanzu basu gama tan-tance adadain wadanda harin ya rutsa da su ba, amma dai akwai gawarwaki sama da 50 da ya tabbatar.
Ya ce a yammacin gobe Laraba asibitin zai dakatar da gudanar da ayyukansa, sabida rashin man fetur da ya ke fama da shi.
Shugaban rundunar tsaro ta farin kaya da ke Gaza Ahmad al-Kahlout, ya shaidawa manema labarai cewar Isra’ila ta yi amfani da bama-baman 6 kirar Amurka ne wajen lalata sansanin baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu