Isa ga babban shafi

Halin da ake ciki game da rikicin Gaza

Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya ce Amurka ce ke da hannu dumu-dumu a duk rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman kashe rayukan da basu ji basu gani ba da Isra'ila ke yi a yankin Gaza.

Falasdina sun bar gidajensu bayan da Isra'ila ta yi ruwan Bama-bamai a Gaza, 30 Oktoba 2023.
Falasdina sun bar gidajensu bayan da Isra'ila ta yi ruwan Bama-bamai a Gaza, 30 Oktoba 2023. © Abed Khaled / AP
Talla

Putin ya ce sakamakon ribar amfanin rikicin da Amurka ke samu ne, ya sanya ta ci gaba da rura masa wuta, amma acewarsa babbar hanyar magance rikicin ita ce tabbatar da kasar Falasdinu.

Tsagaita wuta

Fara Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce babu wani zancen tsakagaita wuta a yakin da suke yi a Hamas, wanda ya lakume rayukan mutane da dama.

Kiraye-kirayen tsagaita bude wuta tamkar kira ne ga Isra'ila ta mika wuya ga Hamas. Hakan ba zai  faru ba.

Martanin Israli'a kan bidiyon da Hamas ta saki

Fara Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi Allah wadai da abinda ya kira da 'farfaganda', bayan sakin wani faifan bidiyo na Hamas ta yi a Litinin din nan, inda ta nuna wasu mutane uku da mayakanta suka yi garkuwa da su a hare-haren su na ranar 7 ga Oktoba.

Fara ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Fara ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. via REUTERS - POOL

A wata sanarwar da ofishinsa ya fitar, ya ce akwai kimanin 'yan Isra'ila 239 da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su a cikin kasar, don haka ya sha alwashin kubutar da su da kuma dawo da su gida.

Bangaren Falasdinawa

A cikin sa'a guda, kauyen Bedouin na Wadi al-Seeq da ke gabar Yamma da Kogin Jordan ya kasance ba kowa, bayan da mazaunansa su kimanin 200 su ka tsre da kafa tare da dabbobinsu.

Sun ce tun a ranar 12 ga watan nan, kwanaki biyar ke nan bayan fara rikicin Hamas da Isra’ila, wasu ‘yan kasar Isra’ila su ka yi musu dirar mikiya wasu daga cikinsu sanye da kayan sarki, suka ba su umarnin ficewa daga kauyen cikin sa’a guda.

Toh sai dai sojojin Isra’ila ba su ce komai kan batun ba, duk kuwa da tuntubarsu da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP yayi.

Batun fargabar da ake yi na bazuwar yakin Isra’ila da Hamas a gabas ta Tsakiya

Fara ministan rikon kwaryar Lebonon Najib Mikati, ya ce ya na yin duk abinda ya kamata don ganin yakin Isra’ila da Hamas bai yadu a cikin kasarsa ba, duk da cewa kungiyar Hezbollah da Isra’ila na musayar wuta a kan iyakar kasashen biyu.

Fara ministan Lebonon Najib Mikati.
Fara ministan Lebonon Najib Mikati. AP - Hussein Malla

A shekarar 2006, an gwabza rikici tsakanin Isra’ila da kungiyar Hzbollah, inda sama da mutane dubu daya da 2 suka mutu daga bangaren Lebanon yawancinsu fararen hula, yayin da a bangaren Isra’ila aka kashe mutane 160 yawancinsu sojoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.