Isa ga babban shafi

Halin da ake ciki game da rikin Isra'ila da Hamas a Gaza

A lahadin nan ne aka cika rana ta 23 da Hamas ta kai harin bazata cikin Isra’ila, wanda kasar ta ce ya kashe mutane mutanenta dubu daya da dari 4 kuma yawancinsu fararen hula ne.

Wani bangare na Khan Younis, da Isra'ila ta kaiwa hari ta sama a yau 29 ga watan Oktoban 2023.
Wani bangare na Khan Younis, da Isra'ila ta kaiwa hari ta sama a yau 29 ga watan Oktoban 2023. REUTERS - MOHAMMED SALEM
Talla

Toh sai dai ma’aikatar kula da harkokin kiwon lafiyar Gaza ta ce, tun daga ranar 7 ga watannan watan da Isra’ila ta kaddamar da hare-haren ramuwar gayya kan Falasdinawa, sama da mutane dubu 8 suka rasa rayukansu yabinsu kuma yara ne.

Bari mu yi duba kan wasu abubuwa biyar da suka faru game da rikicin a cikin sa’oi 24 da suka gabata.

Gargadin Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa an fara sabawa doka da tsarin zaman lafiya, bayan dubban mutane sun fasa rumbunan adana kayan abinci da cibiyoyin rarrabasu da ke tsakiya da kuma kudancin Gaza, inda suka kwashe alkama da filawa da sauran kayayyakin bukatu na yau da kullun, kamar yadda shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinawa Thomas White ya bayyana.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. AP - Niranjan Shrestha

Majalisar ta ce tun bayan faro rikicin, manyan motocin da ke dauke da kayan agaji 84 ne kadai suka samu shiga yankin Gaza, idan aka kwatanta da motoci dari 5 da ke shiga a kowace rana gabanin faro rikicin, lamarin da White ya ce akwai bukatar yin duba akai.

Karuwar kwararar sojojin Isra’ila a Gaza

Isra’ila ta ce ta kara yawan sojojinta a Gaza a cikin dare, bayan da Fara ministan kasar Benjamin Netanyahu ya yi gargadin cewar yakin zai dauki lokaci ana yi kuma yana da wahala.

Sojojin Isra’ila sun ce sun kai wa Hamas hai fiye da sau dari 450 a jiya, ciki harda wanda suka kai kan manyan cibiyoyin Hamas, da huka hada da na harba makamai masu linzaminta.

Wasu daga cikin tankokin yakin Isra'ila akan iyakarta da Gaza.
Wasu daga cikin tankokin yakin Isra'ila akan iyakarta da Gaza. AFP - FADEL SENNA

Ministan tsaron kasar Yoav Gallant ya ce dole ne a tilastawa Hamas ta koma teburin tattaunawa kan mutanen da ta yi garkuwa da su, inda ya ce yawan farmakin da ake kaiwa Hamas ne kadai zai kara bada damar ta amince da hakan.

Musayar fursunoni

A jiya Asabar ne dai shugaban kungiyar Hamas Yahya Sinwar ya ce a shirye suke da batun musayar fursunoni da Isra’ila, ba tare da wani bata lokaci ba, don sakin dukkanin Falasdinawan da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila.

Jagoran kungiyar Hamas Yahya Sinwar.
Jagoran kungiyar Hamas Yahya Sinwar. REUTERS/Mohammed Salem/File Photo

A cewar wata kungiyar Falasdinawa da ke fafutukar kubutar da ‘ya’yansu da ake tsare da su a Isra’ila, akwai Falasdinawa dubu 5 da da dari 2 a gidajen yarin kasar, daga cikin wancan adadi kuma dari 559 na fuskantar hukuncin daurin rai da rai ne.

Maido da hanyoyin sadarwa a Gaza

Da sanyin safiyar Lahadin nan ce hanyoyin sadarwa na Internet suka fara dawowa yankin Gaza, bayan kwashe kimanin sa’oi 36 da akayi babu, sakamakon ruwan bama-bamai da Isra’ila ke yi a yankin.

Yadda hare-haren Isra'ila suka yiwa yankin Gaza.
Yadda hare-haren Isra'ila suka yiwa yankin Gaza. AP

Da misalin karfe 4 na sifiya agogon yankin ne dai ma’aikacin Kamfanin Dillancin Labaran AFP a Gaza, ya ce network din wayarsa ya dawo harma ya samu ya tuntubi wasu mutane da ke kudancin Gaza.

Illolin yakin a yankin Gabas ta Tsakiya

Shugaban Iran Ebrahim Raisi, ya ce hare-haren bam da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa Gaza, na iya tilastawa kasashen yankin daukar mataki, a wani sabon gargadin da ke nuna cewa rikicin na iya bazuwa a yankin baki daya.

"Laifukan gwamnatin da ke kare Yahudawa da kasarsu sun wuce makadi da rawa, kuma hakan na iya tilasta kowa ya dauki mataki,".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.