Isa ga babban shafi

Halin da ake ciki a yakin Isra'ila da Hamas a Gaza

Mahukunta a Zirin Gaza sun ce, an katse hanyoyin sadarwar intanet da na wayoyin salula a daidai lokacin da Isra'ila ta ce, za ta zafafa hare-harenta ta kaza a Gazar a cikin wannan dare na Juma'a.

Yadda hayaki ya turnuke sararin samaniya a yakin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas.
Yadda hayaki ya turnuke sararin samaniya a yakin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas. © AFP - JACK GUEZ
Talla

Batun shigar da kayan agaji zuwa Falasdinwa faraen hula da suka tagayyara sakamakon hare-haren bam ta sama da Isra’ila ke kaiwa a sassan Zirin Gaza na ci gaba da daukar hankali, inda a yau Philippe Lazzarini, shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya, ya koka kan cewar, adadin motocin agajin da ake baiwa damar shiga Gaza bai taka kara ya karya ba. 

Shakku kan alkaluman mutane da suka mutu a Gaza 

Ma'aikatar Lafiyar Yankin Gaza ta wallafa sunayen dubban Falasdinawa da Isra’ila ta kashe. Matakin dai ya biyo bayan shakkun da shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana kan adadin mamatan da ma’aikatar lafiyar ta bayyana. 

Sai dai yayin mayar da martani ga shugaban na Amurka, Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Human Rights Watch sun ce ko kadan babu shakku a kan alkaluman Falasdinawa da suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila. 

Ya zuwa wannan Juma’a, Falasdinawa 7,326 ciki har da kananan yara sama da dubu 3, Isra’ila ta hallaka a matsayin ramuwar gayya kan farmakin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba, yayin da ya zuwa yanzu, Isra’ilar ta rasa mutane sama da 1, 400, ciki har da sojojinta akalla 300. 

Halin da ake ciki kan tattaunawar tsagaita wuta a Gaza 

Bayanai daga Qatar sun ce, tattaunawar neman kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da kasar ke jagoranta tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ta yi nisa kuma akwai alamun nasara. Wasu majiyoyi sun ce akwai yiwuwar Hamas ta sako mutanen  da ta yi garkuwa da su, amma bisa sharadin tilas sai Isra’ila ta dakatar da hare-haren da ke rutsawa da fararen hula. 

Hamas ta musanta mayar da asibitoci sansani 

Kungiyar Hamas ta yi watsi da zargin da Isra’ila ta yi mata nayin amfani da asibitoci a matsayin sansanonin kaddamar hare-hare da makaman roka. 

Daya daga cikin manyan jagororin tsagin siyasar kungiyar ta Hamas, Izzat al-Rishq, ya ce Isra’ila na son fakewa da zargin da ta yi musu ne domin kaddamar da karin munanan haren-hare kan fararen hular da ke samun mafaka a cibiyoyin lafiya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.