Isa ga babban shafi

Najeriya da wasu kasashe sun kada kuri'ar amincewa da tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Hamas

Najeriya tare da wasu kasashe 119 suka kada kuri'ar amincewa da tsagaita bude wuta a rikicin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas.Hakan ya biyo bayan gazawar daftarin kudurori guda hudu a kwamitin sulhu na Majalisar Dimkin Duniya.

Taron Majlisar Dimkin Duniya a kan rikicin Gabas ta Tsakiya
Taron Majlisar Dimkin Duniya a kan rikicin Gabas ta Tsakiya AP - Mary Altaffer
Talla

A babban taron Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma'a, yayin da kasashe 120 suka kada kuri'ar amincewa, 14 ciki har da Amurka da Isra'ila suka kada kuri'ar kin amincewa. Kasashe 45 ne suka kaurace wa zaben.

Kudurin ya kasance kan "kare fararen hula da kuma kiyaye hakkin doka da na jin kai".

Majalisar ta  bukaci dukkan bangarorin da su “ba tare da bata lokaci ba su yi amfani da dokokin kare hakkin bil’adama da na kasa da kasa, “musamman dangane da kare fararen hula.

Yankin Zirin Gaza
Yankin Zirin Gaza REUTERS - REUTERS TV

Dubban fararen hula ne aka kashe a Isra'ila da Gaza, yayin da na baya-bayan nan ke samun karin asarar rayuka sakamakon hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke kaiwa.

Sama da 'yan Isra'ila 1,400 aka kashe a wannan harin. Tun daga wannan lokaci Isra'ila ta shelanta yaki da kungiyar tare da mazauna Zirin Gaza a karshen mako. Sama da mazauna Gaza 7,000 ciki har da yara kusan 3,000 ne aka kashe a hare-haren ta sama, a cewar alkaluman hukuma.

Bugu da kari, kudurin ya yi kira da a ba da kariya ga ma'aikatan jin kai da cibiyoyin jin kai don ba da dama da kuma saukaka ayyukan jin kai na samar da kayayyaki da ayyuka masu mahimmanci don isa ga dukkan fararen hula da ke bukata a Zirin Gaza.

Farmakin Isra'ila a yankin Zirin Gaza
Farmakin Isra'ila a yankin Zirin Gaza © Ohad Zwigenberg / AP

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasdinu ta ce, tun bayan barkewar rikicin, an kashe akalla ma'aikatan jin kai 53 a Gaza.

Da take nuni da Isra'ila a matsayin "Mallaka", Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci ta soke umarnin ficewa daga kasar. Isra'ila ta umarci Falasdinawa da ke arewacin Gaza da su kaura tare da kaura zuwa kudancin kasar amma ta ci gaba da kai hare-hare a yankin.

“Majalisar ta kuma yi kira da a gaggauta sakin fararen hula da ake tsare da su ba tare da wani sharadi ba, tare da neman kare lafiyarsu da jin dadinsu da mutunta hakkinsu bisa bin dokokin kasa da kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.