Isa ga babban shafi

Ayyukan agaji na ci gaba da rauni a Gaza saboda hare-haren Isra'ila

Ayyukan agaji na ci gaba da ja baya a Gaza dai-dai lokacin da bayanai ke nuna cewa cibiyoyin lafiya a Gaza ka iya rufewa matukar ba’a sami agajin man fetur na gaggawa zuwa yammacin yau Laraba ba.

Har yanzu dai babu tabbas game da fara shigar da man fetur Zirin Gaza
Har yanzu dai babu tabbas game da fara shigar da man fetur Zirin Gaza REUTERS - VIOLETA SANTOS MOURA
Talla

Wannan fargaba na zuwa ne dai-da lokacin da wasu karin motoci 20 dauke da kayayyakin agaji daga Masar suka isa Gaza, sai dai a yanzu babban abin bukata shi ne man fetur da za’a yi amfani da shi wajen kunna injina a asibitoci.

To amma tuni majalisar dinkin duniya ta bakin kakakinta Stephane Dujarric ya shaidawa manema labarai cewa akwai manyan tankoki makare da man fetur da ke tsaye a mashigin Rafaa, inda suke jiran umarnin shiga Gaza, sai dai bai yi karin haske kan dalilin da ya hana su fara tafiya ba.

Bayanai na nuna cewa hare-hare ba kakkautawa da Isra’ila ke ci gaba da kaddamarwa a Gaza sun raunata shigar da kayan agaji da aka fara a karshen makon da ya gabata, yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar sakamakon shirin Isra’ila na kutsawa Gazan ta kasa.

Rahotanni na nuna cewa a yanzu jama’a na samun mafaka ne a asibitoci, kuma nan din ne dai ake kulawa da marasa lafiya, abinda ke zama barzana ga barkewar cututtuka, baya ga rashin tabbas da ake da shi, kan cewa Isra’ila ka iya afkawa asibitin, kamar yadda ta faru ‘yan kwanaki da suka gabata.

A gefe guda kuma masu aikin ceto na ci gaba da zakulo gawarwakin jama’a a karkashin baraguzan gine-ginen da Isra’ila ta ruguza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.