Isa ga babban shafi

Asibitocin Gaza sun kusa daina aiki saboda rashin fetur

Ma’aikatar Harkokin Lafiyar Gaza ta yi gargadin cewa sauran asibitocin da suka rage wadanda ake kula da marasa lafiya na gab da daina aiki saboda karancin man fetur din da ake kunna injina da shi. 

Wani asibiti a Gaza
Wani asibiti a Gaza AP - Ali Mahmoud
Talla

 

Jami’an lafiya sun yi hasashen cewa man da ya rage a yankin da za a iya amfani da shi a cikin injinan ka iya karewa cikin san’o’i 48 masu zuwa, abin da ke nufin za a samu kari kan cibiyoyin lafiya 38 da suka daina aiki saboda karancin wutar lantarki. 

Mai magana da yawun ma’aikatar lafiyar Asharaf Al-Qudra ta cikin wata gajeruwar sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Telegram ya koka kan yadda shigar da kayayyakin agaji Gaza ke tafiyar hawainiya. 

A jiya Litinin ma’aikatar ta ce, rashin wutar lantarki da karancin man fetur ya tilasta kulle wasu cibiyoyin lafiya 38, abin da ke nufin za a samu karin masu mutuwa sanadin hare-haren Isra’ila. 

Ma’aikatar lafiyar ta bukaci kungiyoyin bada agaji da Majalisar Dinkin Duniya su gaggauta sanya idanu wajen ganin an kauce wa matsalar karancin man fetur din da ka iya tilasta kulle baki daya cibiyoyin lafiyar da ake da su a yankin. 

Wasu faya-fayan bidiyo sun nuna yadda ake kulawa da marasa lafiya da fitilar kwai, yayin da ake kunna inji kadai idan bukatar gaggawa ta taso, duk da dai an sami rahoton komawar wutar lantarki ta ‘yan sa’o’i kafin daga bisani ta sake daukewa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.