Isa ga babban shafi

Hamas ta zargi Isra'ila da kashe fararen hula 80 cikin daren jiya kadai

Gwamantin Hamas ta sanar da cewa mutuwar farar hula 80 cikin daren jiya kadai a wani hari da ta Isra’ila ta kai.

Wasu daga cikin makamai da Isra'ila ke ci gaba da jibgewa a kan iyakar Gaza
Wasu daga cikin makamai da Isra'ila ke ci gaba da jibgewa a kan iyakar Gaza © Ariel Schalit / AP
Talla

Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar tace harin da ya kare kakaf kan farar hula ya jikkata daruruwan mutane.

Ma’aikatar lafiyar Hamas ta ce kawo yanzu Falasdinawa 5,791 sun mutu a sanadin hare-haren Isra’ila da ta faro tun ranar 7 ga watan Octoban da muke ciki, yayin da 1,400 suka mutu a bangaren Isra’ila, kuma duk mace-macen bangarorin biyu mafi yawa fararen hula ne.

Sai dai kuma rundunar sojin Isra’ila ta ce harin na tsakar daren jiya ya shafi dakunan da Hamas ke amfani da su wajen taron bita kan dabarun yaki da wani sashe na inda take adana makamai.

Harin ya kuma shafi wani bangare na ramukan karkashin kasa da mayakan na Hamas ke buya a cikin su, da shalkwatar rundunar soji, da kuma wajen adana na’urorin harbo makami masu linzami.

Bayanai sun nuna cewa Isra’ila na ci gaba da jibge manyan makamai a kan iyakar ta da Gaza a cigaba da shirye-shiryen da ta ke yi na kutsa kai ta kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.