Isa ga babban shafi

Hare-haren Isra'ila na ci gaba da zafafa a Gaza

Yayin da Isra’ila ke ci gaba da ruwan wuta a Zirin Gaza bayanai na cewa har yanzu akwai alamun kasar ta yi burus da kiraye-kirayen kasashen duniya, inda ta ke ci gaba da kai hare-haren da ke shafar fararen hula kai tsaye.

Har yanzu fararen hula ne suka fi jin jiki a wannan rikici da ake tafkawa
Har yanzu fararen hula ne suka fi jin jiki a wannan rikici da ake tafkawa AFP - MAHMUD HAMS
Talla

A yanzu gidaje sun zamewa jama’ar Zirin Gaza abin tsoro, kasancewar babu wanda ya san lokacin da bam ko kuma makami mai linzami zai iya fadawa.

Bayanai sun ce a wani hari da Isra’ila ta kai yankin cikin daren nan, ta kashe fararen hula 28 wadanda ke cikin gidajen su a yankin Rafah da ke kudancin Gaza.

Duk da kasar na ikirarin kokarin shafe Hamas daga doron kasa ne, amma tuni masu sanya idanu kan yadda wannan yaki ke tafiya ke ganin kaso 70 cikin 100 na masu jin jiki fararen hula ne.

Watakila wannan ce ta sa shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kai ziyara Isra’ila don nuna goyon bayan sa ga kasar dai-dai lokacin da ta ke ci gaba da duba yiwuwar kutsa kai Gaza ta kasa.

Har yanzu dai babu wani shiri na tsagaita wuta, ko kuma kira da ayi hakan da duniya ke yi, illa dai bukatar a Tel-Aviv ta kare fararen hula, yayin da take ci gaba da zafafa hare-hare.

Kawo yanzu yakin da aka shafe fiye da mako biyu ana gwabzawa ya lashe rayukan mutane fiye da dubu 7 a dukannin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.