Isa ga babban shafi

Amurka ta gargadi masu son kaiwa Isra'ila ko Amurkawa hari a Gabas ta Tsakiya

Amurka ta gargadi Iran da kawayenta game da duk wani yunkuri na fadada yakin da Isra’ila ke yi da kungiyar Hamas, sa’o’i kadan bayan da ma’aikatar tsaron Amurka ta dauki matakin kara inganta tsarin sojojinta a yankin gabas ta tsakiya.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a lokacin da yake gudanar da taron manema labarai Tel Aviv, lokacin ziyarar da ya kai Isra'ila.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a lokacin da yake gudanar da taron manema labarai Tel Aviv, lokacin ziyarar da ya kai Isra'ila. via REUTERS - POOL
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a yayin wata ganawa da yayi da manema labarai, ya ce akul wata kasa ko kungiya ta yi amfani da rikicin na Isra’ila da Hamas wajen kaiwa Isra’ila ko kuma Amurkawa hari.

Blinken ya ce Amurka, wacce ta aike da jirajen ruwa biyu na yaki zuwa gabashin tekun Mediterrenean, za tayi dukkanin mai yuwuwa don tabbatar da cewa ta basu kariyar da ya kama.

Kalaman nasa sun tabbatar da jawabin da sakataren tsaro kasar Lloyd Austin yayi tun da farko, wanda yayi kashedin game da kai zafafan hare-hare kan sojojinsu a yankin gabas ta tsakiya.

Akwai dai fargabar cewa mayakan Hizbullah da sauran wasu kungiyoyi da ke samun goyon bayan Iran, na iya amfani da rikicin zirin Gaza domin kaiwa sojojin Isra'ila hari, lamarin da Austin ya ce duk wata kungiya ko kasa da ta aikata hakan ta kuka da kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.