Isa ga babban shafi

Isra'ila ta umarci Falasdinawa fiye da miliyan 1 su gaggauta ficewa daga Gaza

A yau Juma’a rundunar Sojin Isra’ila ta umarci ilahirin fararen hular da ke arewacin Zirin Gaza, ciki har da jami’an Majalisar Dinkin Duniya da su gaggauta ficewa daga yankin zuwa kudanci, nan da sa’o’i 24 don tsira da rayukansu, lamarin da ke sanya fargabar yiwuwar dakarun kasar ta Yahudu su iya kutsawa yankin na Gaza ta kasa. 

Dandazon Falasdinawa tare da mayakan Hamas a yankin Nablus na Gaza.
Dandazon Falasdinawa tare da mayakan Hamas a yankin Nablus na Gaza. AP - NASSER ISHTAYEH
Talla

Wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron Isra’ila ta yi kira ga ilahirin fararen hular yankin arewacin Gaza su gaggauta barin gidajensu zuwa kudancin Wadi Gaza, kamar yadda ta nuna a taswirar yankin da ta wallafa, tana mai cewa ya zama wajibi su bi wannan umurni don kare rayukansu. 

Sanarwar ta ce kungiyar Hamas ta kadamar da yaki a kan Israila, kuma yankin Zirin Gaza ne filin daga, inda ta ce mayakan Hamas ke boye a cikin karkashin kasa a yankin, saboda haka ta ke shaidawa fararen hula cewa barin yankin mataki ne na kare kai. 

Wata sanarwa da ta samu sa hannun kakakin Majalisar Dinkin Duniya, Stephane Dujarric a Juma’ar nan ta ce ta samu labarin wannan umurni na Isra’ila, ta na mai cewa ba zai yiwu mutane sama da miliyan 1 su bar wannan yanki ba tare da an fuskanci gagarumin matsalar jinkai ba. 

A nata bangaren, kungiyar Hamas, mai iko da Zirin Gaza ta yi watsi da wannan umurni, wanda ta bayyana a matsayin farfaganda mara amfani, kana ta yi kira ga Falasdinawa su yi watsi da umurnin na Isra’ila. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.